Uncategorized

Karancin Kudade Ne Yasa Aka Cire Tallafin Mai, Inji Gwamnatin Tarayya.

Spread the love

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, karancin kudade ne yasa ba za a iya ci gaba da biyan tallafin mai ba, sakamakon matsalolin tattalin arziki da cutar corona ta haifar wa kasar.

Karamin ministan albarkatun mai, Timipre Sylba ne ya bayyana hakan, inda ya ce: gwamnatin tarayya ta dakatar da biyan kudaden tallafin mai ne domin ta hade ayyukan hukumar da ke kayyade farashin mai (PPPRA) da kuma hukumar da ke kula da daidaita asusun albarkatun mai (PEF).

Ministan ya jadda cewa, gyara bangaren mai da cire tallafin mai ba siyasa ba ne, an yi hakan ne domin Najeriya ta samu rarar kudade wadanda suka kai naira tiriliyan 1 wanda aka gabatar tun a cikin watan Maris ta shekarar 2020.

Ya ce, “yana da matukar mahimmanci kasar ta dakatar da biyan tallafin mai domin samun damar gyara fannin mai. Gwamnatin ta dakatar da biyan kudaden tallafin mai ne, domin tsare ‘yan Nijeriya daga ‘yan kasuwa masu sha’awar cin kazamar riba a cikin harkokin kasuwancinsu na mai.

Ya kara da cewa, a yanzu haka yawan kudaden da gwamnati take samu ya yi matukar raguwa, ya zama wajibi gwamnati ta dakatar da biyan tallafin mai, inda yace daga lokacin da gwamnati ta dakatar da biyan tallafin mai, an samu rarar kudade wanda ya kai na naira biliyan 500 yanzu haka.

Daga Haidar H Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button