Kwanaki ka’dan suka rage Matsalar Rashin tsaro ya zama tarihi a Nageriya ~Cewar Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kwarin gwiwar cewa duk wasu al’muran da ke jawo mana ciwo da Tashe tashen hankula Nan ba da jimawa ba za su zama tarihi”.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a cikin sakonsa na Kirsimeti a Lokacin da ya ke taya murna ga Kiristocin Najeriya yayin da suke hada kai da ’yan uwa a duk fadin duniya domin murnar wannan buki
Jami’an tsaron mu masu jajircewa, tare da taimakon da ya kamata daga wannan gwamnati, kullum suna fuskantar miyagu a cikinmu, wadanda ke ci gaba da barazana ga zaman lafiyar kasa.

Kwanan

nan, yayin ganawar da takwarorinmu shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS, na tattauna kan bukatar kara kaimi wajen tunkarar wannan matsalar da ke haddasa rashin zaman lafiya a yankinmu.

“Kirsimeti lokaci na bege dasake farfaɗo da kauna, zaman lafiya, farin ciki, soyayya sune jigogi masu maimaitawa na wannan lokaci. A cikin kunci ne jarrabawar al’umma ta hakika ta fito. Ina kira ga ’yan Najeriya da su yi kira ga ruhin zaman lafiya.

“Wannan gwamnatin ba za ta yi watsi da alkawurran da ta yi wa ‘yan Najeriya na samar da ingantacciyar rayuwa ba. Bambance-bambancen tattalin arzikin da aka fara yana haifar da ‘ya’ya. Za mu ci gaba da samar da damammaki ga matasan mu masu yawan gaske don isar da kuzarin da suke da shi.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *