MAULUD: Fasto Yohanna Buru ya jagoranci mabiyansa zuwa mambari domin taya al’ummar Musulmi murnar Mauludin Annabiﷺ a Jihar Kaduna.

Kiristoci a Jihar Kaduna sun taya Musulmi murnar Mauludin Annabi (SAW).

Mabiyan addinan biyu sun tattaru ne a filin wasa na Rachers Bees dake birnin Kaduna, bayan da Kiristocin suke riski Musulman domin taya su murna.

Shugaban Cocin CEIFM dake yankin Sabon Tasha mai suna, Fasto Yohanna Buru shine ya jagoranci tawagar ta Kiristoci izuwa dandalin da ake gudanar da shugulgulan Mauludin a yammacin yau Talata.

Yayin zantawa da manema labaru, Fasto Yohanna ya bayyana cewa ya cancanta kowanne mutum yayi murna da zagawowar ranar haihuwar Annabi Muhammad, kuma ba tare da yin la’akari da al’ada, addini, launin fata ko yankin da ya fito ba. Saboda tarihi ya bayyana ƙarara cewa Annabi zaman lafiya da son juna ya koyar.

Ya

kuma ƙara da cewa, a matsayinsa na Shugaban Kiristoci, zuwa tare da halarta wurin Maulidi baya nufin cewa shi ba mabiyin addini Kiristanci bane. Domin kuwa akwai dubunnan Musulman da suke zuwa Mujami’u duk shekara domin taya mu murna yayin bikin Kirsimeti da zummar samar da zaman lafiya, fahimtar juna a tsakaninmu.

A gefe guda ya tunasar cewa da Musulmi da Kirista duk ƴaƴan Adam ne, saboda haka ƴan uwan juna ne, kuma kowanne ya yarda zai mutu don haka dole muso juna.

A ƙarshe, Fasto Yohanna yayi kira ga ɗaukacin al’ummar Musulmi da Kirista akan suyi amfani da wannan loƙaci wajen ɗabbaka zaman lafiya, son juna tare da addu’ar cigaba ga ƙasarmu Nigeria.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *