RA’AYI RIGA: Banga Dalilin Daya sa ɗan Talaka Zaiyi Murnar Zagayowar ranar ƴancin Kai na Najeriya ba — Matashi Saifullahi Alhaji Saleh Kafin Malamai.

Wani matashi mai suna Saifullahi Alhaji Saleh Kafin Malamai, yace atafau shidai baiga dalilin da yasa talakawan Najeriya zasu dinga yin murnar samun ƴancin kan Najeriya ba, saboda wasu hujjoji daya zayyana. Mu saurari saifullahi:

“Ni Anawa Ra,ayin Banga Dalilin Dayasa Dan Talaka Zaiyi Murnar Zagayowar ranar Samun Yancin Kai na Najeriya ba (Happy Independent), Domin Kuwa Babu Wani yanci Da Talakan Nageria Yasamu A Wannan Halin Damuke Ciki.

Saifullahi

Alhaji Saleh Kafin Malamai ya ƙara da cewa:

“A Maganar Gaskiya Cin Fuskane Dan Talaka Kamata Yayi Murnar Samun Yancin Kai, Domin Kuwa Wallahi Damu Da Waɗanda Basuda ƴancin Kai Bamuda Maraba.

“Duk Wata Wuya Da Marasa Yancin Kai Sukesha Babu Wadda Talakan Nageria Bayasha, Idan Kuma Kana Kaga Mutum Yana Murnar Yancin Kai Kuma Dan Talaka To Gaskiya Ya Kamata A Daukeshi Akaishi Inda Aka Gwada Lafiyar Abdul, Jabbar.

“Ma’ana Aduba Lafiyar Kwakwalwarsa, Domin Kuwa Suma Sunnuna Alamu Na Hauka Tubiryan.

“Idan Kuma Akwai Dan Talaka Mutum Daya Dayake Daja Akan Kalamaina, Bance Yayan Masu Hanu Dashuniba Yayan Talaka Kamata Nace, Toya Futo Yayi Inkari Kuma Ya Kawo Hujjarsa Wacce Take Ingantacciya Akan Kare Kansa Dacewa Yadace Yayi Murnar Samun Yancin Kai”.

Ko me zaku iya cewa, dangane da wannan ra’ayin na Saifullahi Alhaji Saleh Kafin Malamai.?

Ku bayyana mana ra’ayin ku!

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *