Wani tsoho mai shekaru 71, ya mutu a yayin da yake lalata da wata karuwa.

Wani tsoho mai shekaru 71, Ajibola Olufemi Adeniyi, ya mutu a yayin da yake lalata da wata karuwa a ranar Litinin a jihar Ogun.

Lamarin ya faru ne a wani otal da ke unguwar Ogijo a karamar hukumar Sagamu inda mutumin ya je otal din don “hutawa” tare da karuwar mai suna Joy.

Wani mazaunin unguwar da Otal din yake ya shaidawa majiyarmu ta Dailytrust cewa, “A yayin da suke saduwa, mutumin ya fadi ya mutu nan take kuma yan sanda daga sashen Ogijo sun ziyarci wurin, sun karbi katin ATM da lasisin tuki sannan suka kwashi gawar suka ajiye a dakin ajiye gawarwaki na Babban Asibitin Sagamu, yayin da aka kama karuwar. ”

Da

aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace,“ Iyalan mamacin sun roke mu cewa ba sa son batun a kafafen yada labarai. ”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *