Wasu Kungiyoyin raya al’adu a Jihar Benue sunyi kira ga Gwamnatin tarayya da ta kama Shugabannin Kungiyar Miyetti Allah kautal hore.

Manyan Kungiyoyin raya al’adun na Jihar Benue sun roki Gwamnatin tarayya da ta kama Shugabannin Kungiyar Miyetti Allah kautal hore domin Gwamnatin ta nuna adalci game da kamun Shugaban Kungiyar ‘Yan Asalin kabilar Ibo masu yunkurin kafa Kasar Biafara Nmdi Kanu.

Kiran wanda ke dauke da sa hanun Shugabannin kungiyoyin uku wato: Mdzogh U Tiv(MUT), da CP Lorbee(rtd) da AVM Tony Adokwu retired da kuma Dr. Ben Okpa, ta bayyana cewa kiran ya biyo bayan kamun da Gwamnati ta yiwa Nnamdi Kanu Shugaban Kungiyar ‘yan tawayen Biafara.

“Hakika mun yabawa Gwamnatin tarayya a kokarin da tayi na kamo Nnamdi Kanu kuma muna tabbacin cewa Gwamnati za ta adalci akan wannan batu domin tabbatar da zaman lafiya a kasar mu.

“Kamar

yadda muka yabawa Gwamnatin tarayya kan wannan kokari, hakanan kuma muna jawo hankalin Gwamnatin game da sha’anin barazanar tsaro da karancin abinci wanda hakan ke faruwa sakamakon ayyukan Fulani makiyaya da masu daukar nauyin su.

“Mun damu matuka ganin Gwamnatin tarayya batayi wani hobbasa ba domin kama Shugabannin Kungiyar Miyetti Allah da sauran Kungiyoyin ta’addan Fulani makiyaya ba wadanda kai tsaye suke barazana ga tsaro a fadin Jihar da sauran Jihohi.

“Idan har karfin da akayi amfani dashi wajen kama Nnamdi Kanu baza ayi amfani dashi ba wajen kama ‘yan ta’addan dake yawo a titunan Abuja da sauran birane ba” Akwai ayar tambaya kenan inji Kungiyoyin.

Kungiyoyin sunyi zargin cewa a Jihar Benue fiye da kaso 95 cikin 100 na tashe-tashen hankula da ake samu na matsalar tsaro da karancin abinci Fulani makiyaya ne ke haddasa su.

“Munyi mamaki matuka da Gwamnatin tarayya tayi kunnen uwar shegu akan wannan sha’anin.

“Muna son ayi adalci! Muna fatan Gwamnatin tarayya zata bada damar ga ‘yan Jiha domin komawa aikin gona don haka matakin farko da yakamata a dauka shi ne a kama Shugabannin Kungiyar Miyetti Allah wadanda suke kai hare-haren kan al’ummar mu ko kuma a umarci Fulani makiyaya da su fita daga Jihar mu, kuma su rungumi tsarin kiwo irin ma zamani” Inji Kungiyoyin.

Kungiyoyin sunyi wannan kiran ne a yau Juma’a 2 ga watan Yuli 2021.

Activist Isma’eel S Jauro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *