‘Yan media a jihar Kaduna Kowa da kowa ya samu kyautar Sanata Malam Uba sani ~Cewar Ibrahim Salisu abubakar.

Da yake rubutu cikin Alfahari Mai nuni da godiya mataimaki na musamman a ga Sanata Malama Uba Sani Ibrahim Salisu Abubakar ya Bayyana Cewa A tarihin jahar Kaduna, babu wani Media Team da takai yawan Media Team na Senata Uba Sani Babu Media Team da suka zauna domin taruka bayan zabe, sun kuma raba kyautattuka ga tawagar membobinsu

A tarihin Kaduna Babu Media Team da gake tallata ayyukan wani dan siyasa bayan zabe kamar Media Team din Sanata Uba Sani.

Babu

wani Media Team a tarihin Kaduna da gungun membobinsu suka anbaci sunan shugaban su sau fiye da dubu Hamisin 50k a cikin dan karamin lokaci kadan kamar Media Team na Sanata Uba Sani.

Babu Media Team da membobinta suka anfana da kyautattuka, tallafi, jari, aiyukan yi kaman Media Team na Sanata Uba Sani.

A yanzu zan iya cewa kusan 90% duk Mambobin Media Team na sanata sun taba anfana da wata kyauta, ko jari ko wata hanya ta taimako..

Wanann duka bai kare ba a kullum Ana cigaba da samun hanyoyi na taimakon mutane wanda suka fito da kan su wajen tallata Sanata Uba Sani…

Ibrahim ya kara da cewa Babu wanda zai iya ma kowa sai Allah amma an kokarta matuka wajen kare darajar yan Media Team na gidan Sanata wanda wasu ma da yawa a dalilin Sanata ne farkon tallata dan siyasa a Media daga wajen su.

Sanata malam Uba Sani shine Sanata mafi gabatar da kudri a majalisar dattijan Nageriya kawo yanzu Sanatan ya gabatar da kudri gaban majalisar sau Ashirin 20 cikin harda wanda shugaban kasa Muhammadu buhari ya rattaba hannu Wanda yanzu haka ya Zama doka a Nageriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *