El-Classico: Magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, sun kaiwa motar mai horarwar su “Koeman” hari.

Koeman

An dai hango magoya bayan ƙungiyar ta Barcelona ne kewaye da motar mai horarwar tasu a lokacin da yake kokarin ya gudu daga filin wasan su na Camp Nou.

Tuni dai Barcelona ta fito ta yi Allah wadai da abinta ta kira da “munanan aika-aika da cin mutunci” da aka yi wa Ronald Koeman a wajen filin na Camp Nou a ranar Lahadi bayan da Real Madrid ta zo har gida tabawa Barcelona kashi da ci 2-1.

class="wp-block-image size-full">
El-Classico

An ga wani Faifan bidiyo da aka ɗauka ne dai, inda a ciki suka kewaye motar Koeman yayin da yake ƙoƙarin ficewa daga harabar a wani yanayi da aka ɗauka a sannan aka saka shafukan sada zumunta na zamani.

Blaugrana sun ce za su aiwatar da matakan kariya nan gaba, don tabbatar da cewa “irin wannan lamari mara kyau bai sake faruwa ba”.

Shin menene yasa mutane suka juya wa Koeman baya?

Lamarin daya faru a yammacin Lahadi ya nuna sabon tashin hankali a yaƙin da wasu magoya bayan Barcelona ke yi na ƙoƙarin ganin an cire Koeman daga muƙaminsa na mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona.

El-Classico

Barcelona tana tsakiyar teburi a gasar La Liga ta bana a karkashin kulawar Koeman kuma ta sha kashi sau biyu 3-0 a gasar cin kofin zakarun Turai ta Champions League.

Rashin nasarar da Real Madrid ta yau, ya tsawaita, kuma shine mafi munin rashin nasara da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona tayi a wasan Clasico na Madrid da Barcelona tun 1965, wanann ya ƙara matsa lamba ga mai horar war na Blaugrana.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *