Fitaccen ɗan wasan Nigeria, Ahmed Musa ya angwance da sabuwar amaryarsa, Maryam.

Fitattacen ɗan wasan Nigeria kuma ɗaya daga cikin zaƙaƙuran ƴan wasan tamaula a Duniya, Ahmed Musa ya angwance da sabuwar amaryasa jiya Lahadi mai suna Maryam a wani biki da ya shammaci Jama’a.

Sabuwar Amarya ta sa wadda ƴar ƙabilar Shuwa ce, ta angwance da Ahmed Musa ne shekaru huɗu bayan auren Juliet Ejue daga garin Ogoja ta Jihar Cross Rivers.

Idan ba’a manta ba, a shekarar 2017 ne Ahmed Musa ya raba gari da tsohuwar matarsa kuma uwar yayansa Jamila Musa.

A yanzu fitaccen ɗan wasan, wanda yake taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Ahmed Musa yana da jumallar mata biyu kenan.

Rahoto

| Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *