Gasar Firemiya ta Najeriya ta dawo, za’a gwabza a sati na ɗaya. Karanta kaji lokacin da Ƙungiyar ka zata kece fafata.

Akwa United (Masu riƙe da kambun gasar yanzu haka)

Bayan dogon hutu da gasar Firemiya ta ƙasa ta shafe, daga ƙarshe dai za’a dawo da taka leda mako bayan mako kamar yadda aka saba a daukacin filayen wasannin ƙwallon ƙafar dake ƙasar nan.

Wasan farko dai za’a buga wasan hamayya ne na kudu maso yamma, tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta MFM da kuma Remo Stars da kimanin karfe biyar zuwa na yamma.

Sauran wasannin da za’a buga sune duka a karfe huɗu na yamma.

class="has-text-align-justify">Kamar wasa na biyu da za’a buga tsakanin Heartland ta garin Owerri da Kungiyar kwallon kafa ta Nassarawa United a can garin na Owerri ƙarfe hudu shima.

Wasa na uku kuwa, Akwa United ce dake riƙe da kambun gasar ta NPFL zata karɓi bakuncin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars daga Kano, ƙarfe huɗu.

Yan wasan ƙwallon ƙafar Kano Pillars na murnar zura kwallo a gidan kifi.

Idan za’a iya tunawa ƙungiyar sai masu gida ta samu nasarar lashe kofin da aka kammala na shugaban ƙasa da ya saka a karon farko.

Wanda hakan yasa masana wasanni da dama, suke ganin cewa za’a kai ruwa rana da kungiyar, musamman ma naɗin da suka yiwa Salisu Yusuf a matsayin mai horar war ta (4pm)

Katsina United zata amshi bakuncin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enugu Rangers ne. (4pm)

Sai kuma Sunshine Stars da zata goge raini ita ta Wikki Tourist ta garin Bauchi. (4pm)

Daga garin Ilorin kuwa, Kwara United ƙoƙarin doke Kungiyar kwallon kafa ta Dakkada zatayi duk a wannan sati na ɗaya. (4pm)

Bugu da kari, Gombe United da shooting Stars zasu kece raini tsakanin su a can garin na Gombe. (4pm)

Niger Tornadoes kuwa zata so ace tayi wa Plateau United wankin babban bargo ne. (4pm).

Ga cikakken jerin jadawalin wasannin a takaice:

Gasar Firemiya ta Najeriya sati na Ɗaya (2022)

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *