Manchester City zata kara da Tottenham a sabuwar gasar Firimiya ta kasar Ingila ta shekarar 2021/2022

Hukumar shirya gasar Firimiya ta kasar Ingila ta sanar da ranar fara sabuwar gasar ta shekara ta 2021/2022 mai zuwa.

Ta cikin jadawalin sabuwar gasar ya bayyana a ranar 14 ga watan Agusta za’a fara wasannin mako na farko na gasar.

Inda sabuwar gasar ta kunshi sabbin kungiyoyi uku da suka samu damar hawowa gasar da suka hada da Brentford da zata kara da Arsenal, sai kuma
Norwich da Watford da zasu kara da Liverpool Aston Villa.

Haka

zalika hukumar na shirin baiwa ‘yan kallo damar fara shiga filayen wasanni domin kallo muddin masu kamuwa da cutar Covid-19 basu cigaba da kamuwaba a kasar.

Jerin jadawalin wasannin mako na farko a gasar sun gada da

Brentford da Arsenal

Burnley da Brighton

Chelsea da Crystal Palace

Everton da Southampton

Leicester City da Wolverhampton

Manchester United da Leeds United

Newcastle United da West Ham United

Norwich City da Liverpool

Tottenham Hotspur da Manchester City

Watford da Aston Villa

Wasannin dai duka zasu gudana a ranar 14 ga Sabon watn Agusta mai zuwa na shekarar da muke ciki

Rahoto: Ahmad Nakowa

Daga: Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *