Vazquez ya sabunta kwantaragi da Real Madrid duk da ya na fama da rauni

Dan wasan bayan Kasar Andalus(Spain) da Real Madrid Lucas Vazquez, ya sabunta kwantaragi da kungiyar har zuwa shekara ta 2024 kamar yadda tawagar ta sanar a shafinta na Internet a yau Alhamis.

Mai shekaru 29 Vazquez, ba zai wakilci kasar shi a gasar Euro 2020 sakamakom rauni da ya ke fama dashi.

Dan wasan dai ya koma Madrid daga Espanyol a shekaru shida baya da suka gabata.

Haka zalika dan wasa Vazquez kungiyar Bayern Munich da sauran wasu manyan kungoyoyi a nahiyar sunyi zawarcinsa, sai dai tuni ya amince da aiki a Karkashin sabon mai horar da tawagar Carlo Ancelotti.

Ancelotti

dai ya zama kucin Real Madrid sakamakon ajje aiki da tsohon mai horar da kungiyar Zidane da ya yi.

Haka kuma kungiyar ta sayi dan wasan bayan Bayern Munich David Alaba.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *