WASANNI: Akwa United ta lashe gasar Kofin Firimiyar Nigeria karon farko a tarihin ƙungiyar.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Akwa United ta yi nasarar lashe gasar Firimiyar Nigeria wadda ake yiwa laƙabi da NPFL, karo na farko a tarihin ƙungiyar.

Wannan nasara ta tabbata ne bayan samun nasarar da Akwa United ta yi na doke ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta MFM da ci 5-2, wasan da aka buga yau Lahadi a babban filin wasa na Godswill Akpabio dake garin Uyo ta Jihar Akwa Ibom.

Har’ilayau; ƙungiyar ta Akwa United ta zama zakara a kakar wasan bana ne, bayan samun jumullar maki 71 cikin wasanni 37 da ta doka; wanda kuma ake sa ran zata buga wasanta na ƙarshe da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Lobi Stars a ranar Alhamis, 5 ga watan Ogusta 2021.

Rahoto

| Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *