Shari’a Saɓanin Hankali: Kotu ta saki Amaryar Data Sheƙawa Uwargidan ta Ruwan Zafi Tafasasshe.

A wani salo na nuna karin maganar nan ta Shari’a Saɓanin Hankali, wata Kotun majistire mai lamba 24 a jihar Kano, ƙarƙashin mai Shari’a Umma Kurawa, ta saki wata Amarya data ƙona Uwargida da ruwan zafi.

Tunda fari dai an gurfanar da amaryar ne mai suna Hafsah Isa a gaban kotun abisa zargin kwara wa uwargidan ta Ɗaharatu Gayawa tafasasshen ruwa a jikinta, inda nan take ta saɓule gamida ƙone jiki.

class="has-text-align-justify">Lauyan gwamnati, S.A Wali ne ya sake gabatar da ita a gaban kotu, sai dai kuma lauyan dake kareta wato Barrister Nasiru Ahmad ya nemi beli.

Koda neman belin da yayi, Kotu saita amince. Duba da yadda Uwargidan take ta ƙara samun sauƙi.

Daga karshe kotun ta amince abada belin ta abisa sharuɗɗa kamar haka:

  1. Zata Kawo mijinta
  2. Kwamandan Hisba na yankinsu
  3. Likita
  4. Kuma kowanne daga cikin su sai ya ajiye zunzurutun kuɗi har Naira dubu ɗari biyu da hamsin a matsayin wani kandakarki koda zata gudu.
  5. Kowannen su zai kuma kawo shaidar takardar aikin sa.

An kuma daga shari’ar zuwa 17 ga watan Ɗaya, a matsayin ranar da za’a cigaba da gudanar da shari’ar.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *