Wata kotun shari’a ta raba aure a Zamfara, sakamakon ƙarar da wata sabuwar Amarya ta shigar bisa ga girman mazakutar mijinta, tare da cewa baza ta iya zaman aure da shi ba.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Kotun shari’ar dake zaune a unguwar Samaru ƙaramar hukumar Gusau ta Jihar Zamfara ta karɓi koken wata mata mai suna Aisha Dannupawa game da mijin data aura sati guda daya gabata.

Aisha Dannupawa ta bayyana a gaban Ƙotu cewa kwanciyar aure da mijinta tamkar azabtarwa ne duba da girman mazakutarsa.

A cewarta, “a duk loƙacin da ya buƙaci mu kwanta, maimakon samun nishaɗi sai na rinƙa shan wahala kamar za’a cire Rai na. Wannan shine dalilin da yasa nazo gaban Kotu domin bazan iya jure zaman aure dashi ba”.

Daga nan ne kuma mijin Aisha ya amince da kuɗirin da ta kai gaban Kotu, kuma aka raba auren.

Kotu

ta umarce shi ya sake ta kamar yadda Shari’a ta tanadar, amma da sharaɗin zata biya tsohon mijin nata wasu ƙayyadaddun kuɗaɗe tunda yake itace ta nemi ya sake ta.
Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *